Thursday, December 25
Shadow

Abin takaici, Kasar China ce kadai cikin kasashen Duniya ta nuna da gaske tana tare da Najeriya tun bayan Bharazanar Amurka

Rahotanni sun nuna cewa, kasar China ce kadai ta nuna da gaske take tana tare da Najeriya bayan barazanar da kasar Amurka ta yi na shigowa Najeriya dan yakar wadanda ta kira da cewa sunawa Kiristoci Khisan Kyiyashi.

Kasar China ta nuna tana tare da Najeriya ne saboda tana da karfin dangantaka ta tattalin Arziki a Najeriya kuma Amurka zata zo ne dan ta lalata wannan dangantakar.

Abin mamaki shine ko kasar Ingila da ta reni Najeriya bata nuna goyon baya ga Najeriya ba.

Saidai kungiyar hadin kan kasashen Turai EU ta nuna cewa a girmama kasancewar Najeriya a matsayin kasa me zaman kanta, wanda hakan na jeka nayi kane.

Karanta Wannan  Tinubu yayi watsi da Arewa, kudu yake ta rayawa>>Inji Kwankwaso

Kasar Saudiyya da sauran kasashen Larabawa wadanda su ma suna da dangantaka me karfi da kasar Amurka sun kasa fitowa su nuna suna tare da Najeriya duk da yawan musulman dake Najeriya da kuma yanda ake yawan zuwa aikin Umrah da Hajji a Najeriya.

Kasar Faransa itama shirunta ya zowa mutane da mamaki ganin cewa itace babbar kawar shugaban kasa me ci watau, Bola Ahmad Tinubu, Bini-Bini da ya fita kasar waje yana can.

Kasar Rasha ba za’a zargeta da rashin nuna goyon baya ga Najeriya ba saboda a lokacin yakin basasa, Kasashen yamma sun goyi bayan Inyamurai ne a yayin da Rasha kuma ta goyi bayan Najeriya har Najeriya ta yi nasara a yakin.

Karanta Wannan  Yanzu Mace Ba Allura Bace A Cikin Ruwa, Mangoro Ce Akan Faranti Sai Wadda Kake So, Cewar Ummi Ibrahim

Saidai bayan hakan, Najeriya ta sake komawa tana hulda da kasashen yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *