
Yau Litinin, manyan motocin dakon man fetur guda 1,000 mallakin kamfanin Dangote, masu amfani da iskar gas (CNG), sun fara aikin dakon man fetur daga matatar man Dangote zuwa gidajen mai a sassan Najeriya kyauta ba tare da caji ba.
Wannan mataki na daga cikin kokarin rage tsadar man fetur da kuma karancin da ake fuskanta a wasu yankuna. Ana sa ran hakan zai taimaka wajen kara wadatar man fetur da saukaka farashinsa ga ‘yan kasa.
Sai dai, a baya irin wannan yunkuri ya fuskanci turjiya daga wasu bangarori, musamman kungiyar direbobi da kuma dillalan man fetur, wadanda ke ganin hakan na iya shafar sana’arsu.
Yaya kuke kallon wannan mataki na Dangote ko hakan zai taimaka wajen rage wahalar man fetur a kasar nan, ko kuwa akwai wata barazana da ke tattare da hakan ga masu zaman kansu?
Daga Rariya.