
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar Amurka sun mikawa shugaban kasar kalar Hare-haren da suke son kawowa Naira.
Sun mika masa tsare-tsaren hare-haren guda biyu, na farko yanayi ne me tsanani, sai matsaka kaici sai kuma me sauki.
Yanayi me tsanani shine kawo jirgin ruwan yaki na Amurka kusa da Najeriya inda za’a rika aiko da jiragen yaki suna luguden wuta musamman a Arewacin Najeriya.
Yanayi matsakaici shine Amurkar ta rika aiko da jirage marasa matuka da zasu rika kaiwa ‘yan Bindiga hari.
Yanayi me sauki kuma shine goyon bayan sojojin Najeriya da bayanan sirri da kuma aiki tare wajan kaiwa ‘yan Bindigar hari.
Zuwa yanzu dai ba’a san wanne shugaban kasar Amurkar zai dauka ba.