Wednesday, January 15
Shadow

Abubuwan da mata suka fi so

Mata suna son abubuwa da yawa, ga kadan daga cikinsu kamar haka:

Mata na son kyauta: Kyauta na kara dankon Soyayya, kyautar kudi, kayan sawa, Abinci ko wani abin amfani suna daukar hankalin Mata sosai.

Mata na son namiji me kwalliya: Mata nason su ga namiji tsaf-tsaf yana kwalisa, Eh ka yi wanka kasa kaya masu kyau, hula me kyau, takalmi me kyau, zak ga mata na ta kallonka, kuma budurwarka zata so tsayawa tare da kai.

Mata na son namiji me kudi: Kusan dukka mata na son namiji me kudi, dalili kuwa shine su dangin kudi ne, inda ake kyale-kyale da cin me dadi, me babbar mota, me yawan tafiye-tafiye, m rike babbar waya, me yawan kyauta. Kuma karka ga laifinsu, su dama abokan jin dadin rayuwa ne dan haka da kudi sun fi kyawun rikewa.

Karanta Wannan  Saboda matsalar tsaro: Gwamnatin tarayya ta umarci ministan tsaro da shuwagabannin sojoji su koma Sokoto da zama

Shiyasa ma karka ji haushi idan wanda yafi ka kudi ya kwace maka budurwa.

Mata suna son ka nuna ka damu dasu: Mata suna matukar son su ga an nuna ana sonsu, an damu da damuwarsu ana taimaka musu da shawarwari da sauransu.

Mata na son Namiji me basu dariya da debe musu kewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *