
Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Nicolas Felix ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai samu kuri’u Miliyan 15 a zaben 2027.
Yace wannan babu tantama akai.
Ya bayyana hakane a yayin da ya rabawa wasu mabukata man fetur kyauta a Suleja dake jihar Naija ranar Alhamis.
Ya ce Hadakar ‘yan Adawa a ADC ba zata zamarwa Shugaba Bola Ahmad Tinubu barazana ba.
Ya kara da cewa, kamar yanda ‘yan Adawar suka taho suka hadu, haka kuma zasu watse.