
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya bayyana cewa, Kiristoci yafi addinin Musulunci amfana da hutu da ake a tsarin ilimi na Najeriya.
Ya kara da cewa, Ana hutun sabuwar shekara, ana hutun Easter, hakanan ana hutun Kirsimeti sannan kuma tsarin ilimin gaba daya kusan akan tsarin Kiristanci yake amma Musulmai sun hakura suna aiki dashi.
Yace idan kungiyar CAN ta ce zata kai kara, to hakan zai sa suma musulmai su dauki matakin ramuwa, yace idan har CAN tana son ta yi magana akan wannan lamari, roko zata yi ba barazanar zuwa kotu ba.
Yace a kasashen Musulmai, Juma’a ce ake bayar da hutun makaranta dana aiki amma a Najeriya ba haka tsarin yake ba kuma musulmai sun yadda suna amfani da wannan tsari.
Yace kuma turawan mulkin Mallaka ne suka dora mu a wannan tsari, yace kai bari ma kuji, kamin zuwan turawan mulkin mallaka, tsarin shekarar addinin Musulunci ne ake amfani dashi a Najeriya.
Yace kuma magana ta Allah itace, wadannan jihohin da suka bayar da hutu doka a kundin tsarin mulkin Najeriya ta amince musu da yin hakan.
Dan haka yace a kyalesu.