Monday, December 9
Shadow

A yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsin rayuwa, Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 5 wajan gyaran gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 5 daga cikin kudin ‘yan Najeriya wajan gyaran gidan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima dake Legas.

Hakan ya bayyanane a shafin GovSpend wanda shafine dake saka ido kan yanda gwamnatin Najeriya ke kashe kudaden talakawa.

Shafin ya nuna cewa gwamnatin ta kashe jimullar Naira N5,034,077,063 a watan Mayun da September dan gyara gidan mataimakin shugaban kasa dake Legas.

Hakanan Ministan Abuja,Nyesome Wike shima ya bayyana cewa, zasu kashe Naira Biliyan 15 dan ginawa mataimakin shugaban kasar gida a Abuja.

Karanta Wannan  Yanzu Yanzu Gobara ta tashi a kasuwar kantin kwari (Thaiba General Enterprise LTD)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *