Wednesday, January 15
Shadow

Addu’a ga mai ciki: Addu’ar saukin haihuwa

Wannan addu’a da zamu baku anan manyan malamai sunce sadidan ce, an gwada akan mata dake nakuda kuma an yi nasara:

Saidai kamin mu baku wannan addu’a, ga bayani kamar haka:

A binciken masana malamai na sunnah sun ce babu wata addu’a da aka ware wadda aka ce mace me ciki zata rika yi.

Malamai sunce akwai dai hadisan karya da ake dangantawa da Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) akan addu’a ga mai ciki.

Misali Akwai hadisin da aka ce, A lokacin da fatima(A.S) ta zo haihuwa, Ma’aikin Allah Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yasa Umm Salamah da Zaynab bint Jahsh su zo su karanta mata Ayatul Kursiyyu, da kuma al-A‘raaf 7:54, Yoonus 10:3, da kuma falaki da Nasi, Saidai wannan hadisin karyane, domin karin bayani ana iya duba al-Kalim at-Tayyib (p. 161) na Ibn Taymiyah.

Karanta Wannan  Addu'ar biyan bukata cikin gaggawa

Saidai an tambayi Shaykh Muhammad ibn Saalih al-‘Uthaymeen akan addu’ar da za’awa mace me ciki dan ta samu saukin haihuwa.

Sai yace, Bansan wata addu’a ba da ta zo a sunnah ba da aka ce awa mace dan ta samu saukin haihuwa ba.

Ya kara da cewa, saidai idan aka karantawa mace dakw nakuda ayoyi da suka yi magana akan saukaka abubuwa a Qur’ani, kamar al-Baqarah 2:185, da kuma wadda ta yi magana akan haihuwa, watau Faatir 35:11, yace mace zata samu saukin haihuwa da yardar Allah, wannan ba wai bane, an gwada kuma yayi aiki.

Yace duka Qur’ani waraka ne, wanda zai yi wannan karatu da wanda za’awa karatun dole su zama musulmai kuma wanda suka yi imani da hakan cewa zai yi aiko, to Insha Allahu zai yi aiki.

Karanta Wannan  Yadda ake gwajin ciki da gishiri

Kamar yanda Allah madaukakin sarki ke cewa, Kuma mun saukar daga qur’ani wanda warakane kuma rahama ne wanda suka yi imani, kuma baya amfanar da azzalumai komai sai bata. al-Isra’ 17:82.

Wannan aya tana magana akan waraka ta zahiri ta jiki, da kuma waraka ta badili.

Addu’ar uwa akan da, karbabbiyace insha Allah, dan haka uwa ta yawaita yiwa danta dake ciki addu’o’i masu kyau na shigowa duniya lafiya da rayuwa me albarka da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *