Wednesday, January 15
Shadow

Addu’ar barka da safiya


Aminci da yarda ya k’ara tabbata ga mamallakin
zuciyata,
farin wata mai haskaka zuciyata,
kaine
ka zamo farin cikin rayuwa,
ina da tabbacin cewa
zuciyarka tana cike da so na
da bege na acikin wannan sansanyar safiyar
kamar yanda tawa ta kasance haka,
zai zama
abin alfaharina cewa wannan sak’on nawa shine
abu mafi soyuwa daya fara riskarka cikin wannan
ni’imtacciyar safiyar masoyina…
Ina fatan ka tashi lafiya.

Duk sha’aninka na rayuwa, kar ka cire Ubangiji ciki, kana buƙatar Allah a kowannen lokaci.

A ruwaito daga Anas bin Malik (12AH – 93AH) cewa, Manzon Allah ﷺ ya yi Nana Fatima عليها السلام wasici da karanta wannan addu’ar safiya da maraice:

“يا حي يا قيوم برحمتك أستغيث أصلح لي شأني كله ولا تكلني إلى نفسي طرفة عين”

Ma’ana: “Ya Rayayye, Ya Mai tsayuwa da komai! Da rahamarKa nake neman taimako, Ka gyara mini dukkan al’amura na, kuma kada ka bar ni ga kiftawar ido”.

Wannan wuridi ne mai ƙarfin gaske. Wannan addu’a tana daga cikin wurudan safiya da maraice, duba Hisnun Muslim, babi na 27 (babin Zikirin Safiya da Maraice) addu’a mai lamba ta 85.

Karanta Wannan  Addu'a ga masoyiyata

Malamai da yawa sun yi sharhi kan ma’ana da hikimar wannan addu’a kamar Ibn Qayyim Al-Jazawziyya (691AH – 751AH) cikin طريق الهجرتين وباب السعادتين da Imam Al-Manawai (952AH – 1031AH) cikin فيض القدير شرح الجامع الصغير.

A taƙaice, cikin daƙiƙa ɗaya (1 sec), ya za ka yin (kuskuren yin) abin da zai jefa rayuwarka cikin ƙunci, ko ta wasu, ko ka yi kuskuren (abin) da zai bibiyi rayuwarka har mutuwa. A cikin kiftawar ido, za ka iya rasa imaninka (addininka), hankalinka, lafiyarka, dukiyarka, mutuncinka… Kana buƙatar Allah a koda yaushe, kana buƙatar kariyar Ubangiji kodayaushe da sharaɗin, kai ma za ka yi iya bakin ƙoƙarinka na kiyaye iyakokin Allah.

Ya Ubangiji! Ni ma kar ka bar ni da kai na, daidai da kiftawar kwayar ido.

Barka da Safiya
.
Na wayi gari cikin soyayyarki baiwar Allah sannan
na kasance cikin kyakkyawan yanayi sanadin
soyayyar da kike nunamini,
na kasance a
karkashin kulawarki sanadin kaunar da kike bani,

zuciyata takan tsananta tunaninki duk
lokacin da nake maraicin ganinki,

ke ce mai haskamin
gaba a duk sanda Na tsinci kaina cikin duhu,

Karanta Wannan  Sakon rashin lafiya ga masoya

nakan rasa Duniyar da nake ciki
idan har Na tuna da tausasan kalaman bakinki.

Wata Rana ANNABI(S.A.W) Ya Shiga Masallaci, Sai Yayi Kicibis Da Wani Mutumin Madinah Mai Suna;“Abu Umama”, Sai ANNABI(S.A.W)! Ya Ce:
:
“Abu Umama Ya Na Gan Ka a Masallaci a Zaune, Ga Shi Kuwa Yanzu Ba Lokacin Sallah Ba Ne???”
;
Sai Ya Ce:“Ya RASULULLAHI! BAKIN CIKI, Da BASUSSUKA Ne Suka Yi Min Katutu!”
:
Sai ANNABI(S.A.W) Ya Ce:”Me Zai Hana In Koya Maka Wasu Kalmomi, Da In Dai Ka Fad’e Su ALLAH Zai Yaye Maka Bakin Cikin Da Yake Damunka, Kuma Ya Biya Maka Bashin Da Yake Kanka!”
;
Sai Ya Ce:”Godiya Nake Ya MANZON ALLAH!”
:
Sai Ya Ce Masa:“Duk SAFIYA Da MARAICE Ka Ri’ka Lazimtar/Yin Wannan Addu’ar:
:
“ALLAHUMMA INNI A’UZU BIKA MINAL HAMMI WAL HAZANI, WA A’UZU BIKA MINAL AJZI WAL KASALI, WA A’UZU BIKA MINAL JUBNI WAL BUKHLI, WA A’UZU BIKA MIN GALABATIDDAINI WA QAHRIRRIJALI”.
:
Wannan Sahabi – Abu Umama – Ya Ce:“Sai Na Yi Yadda ANNABI(S.A.W) Ya Ce Na Yi, Sai Kuwa ALLAH Ya Yaye Min Bakin Cikin Dake Damuna, Kuma Ya Biya Min BASUSSUKAN Da Suke Kai Na”.

Karanta Wannan  Yadda zaka sa mace tunaninka

ALLAH KA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA, ALLAH YA ‘KARA KARE MU DAGA MASIFAR BASHI DON ALFARMAR SHUGABA(S.A.W).

Barka da safiya kyakyawana

Barka da safiya mijina gari

Inafatan kawayi farar safiya cikin nishadi hadi da jindadi Allah yasa hakan

Hubby inafatan Allah yahadaka da dukkanin Aljairan dakecikin wannan rana Akasin haka takareka

Inamai rokon Allah daya hadaka da dukkanin halak dinka yakuma kiyayeka daga haramin komai.kankantarsa

Allah yakiyaye gabanka dabayanka

Allah kuma yabaka nasara Akan makiyanka

Hubby insanka da dukkanin soyayya

Ina kuma burin kasancewa taka uwar ya yanka

Inada bukatar zama sirika mai kamar “ya Awan iyayenka

Inakuma so naza ma’adanar sirrikanka

Dan haka nake maikara zurfafawa Acikin mastananciyar oaunarka

Hakika kaidin kazama kamar jini wanda keyawo Ajikina

Kafi mastayin ruwa Arayuwata domin ahiruwa zai yi Amafanine idan kana tare dani Akasin haka kuma bazaiyi Amfani Agareniba.

Gaba daya banaso incikaka da surutu shiyasa nake tinani rufe sakona daganan

Inasanka farin cikin kashine burina jindadinka shine fatana saka nishadi kuma mafarkina zama da kai burina

Ina mai rokon Allah takareka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *