Rahotanni daga kasar China na cewa, aikin Ofis yayi karanci a kasar inda matasa da yawa da suka kammala digiri na biyu dana uku watau Masters da PhD sun rungumi kananan sana’o’i irin su tukin motocin haya da aiki a gidajen abinci da saurans.
Rahoton BBC yace wasu masu PhD sun koma aikin goge-goge a ma’aikatu inda wasu ke aikin kai sakonni gidaje.
Wani matashi dan shekaru 25 da majiyar tamu ta yi hira dashi me suna Sun Zhan ya bayyana cewa ya kammala Digirin Masters a fannin Kididdigar kudi, watau Finance inda yayi fatan yin aiki da babban kamfani dake hadahadar kudi ko banki, yace amma ya nemi irin aikin da yake so bai samu ba.
Yace yanzu yana aiki ne a wani gidan abinci dake birnin Nanjing inda yake mikawa mutane irin abincin da suke so idn sun shiga gidan abincin.
Rahoton yace miliyoyin matasa ne a kasar China ke kammala karatun jami’a amma a wasu fannonin babu aikin yi.