Sunday, January 11
Shadow

A’isha Buhari ta sake bayyana wani abin mamaki game da rayuwar Buhari da ya sa mutane rike baki

Matar tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Hajiya A’Isha Buhari ta bayyana cutar da tawa tsohon shugaban Katutu har ya rasu.

Ta bayyana cewa, Shugaba Buhari yana fama da matsalar ciwon Sanyi.

Tace kuma ciwon ya samo asali ne daga aikinsa na soja lokacin yana matashi, suna shiga daji, kaya na bushewa a jikinsa bayan sun jike.

Sannan da sanyin AC, watau na’urar sanyaya daki ga kuma tsufa duk sun tarar masa a jiki.

Hakanan ta kawo cewa, Tsohon shugaban ya sha taba lokacin yana matashi wanda hakan ma ya taimaka wajan rashin lafiyar tasa.

Hajiya A’isha Buhari dai ta yi maganganu da yawa akan Marigayi Shugaba Buhari da suka baiwa mutane mamaki, wasu na ganin cewa bai kamata ta yi su ba.

Karanta Wannan  Gwamnonin Zamfara da Benue sun ƙalubalanci gayyatar kwamitin majalisar wakilai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *