Wednesday, May 14
Shadow

Akpabio zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa jana’izar Fafaroma Francis

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da wata tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar dattawan ƙasar Godswill Akpabio zuwa birnin Vatican domin halartar jana’izar Fafaroma Francis a ranar Asabar 26 ga watan Afrilu.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ta ce tawagar za ta miƙa wata wasiƙa ta musamman da ke ɗauke da sakon jaje daga shugaba Tinubu zuwa ga muƙaddashin shugaban fadar Vatican.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da ƙaramar ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu Ojukwu da Archbishop Lucius Iwejuru Ugorji da Shugaban Majalisar Bishop-bishop ɗin Katolika na Najeriya kuma Babban Bishop na cocin katolika na Sokoto, Archbishop Matthew Hassan Kukah da kuma Archbishop na Abuja, Archbishop Ignatius Ayua Kaigama.

Karanta Wannan  Yanda Sanata Akpabio Ya taba rike hannuna a gaban mijina>>Sanata Natasha Akpoti

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne shugaba Tinubu ya bi sahun mabiya ɗarikar katolika da kiristoci a faɗin duniya domin nuna alhinin rasuwar Fafaroma Francis, wanda ya bayyana a matsayin bawan Allah mai mai matuƙar tausayin talakawa, kuma wanda kasance abin koyi ga miliyoyin mutane a duniya baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *