
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar cewa su raba kafa, kada su tsayawa sana’a daya.
Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na ChannelsTV.
Yace ba zai yiyu mutum ya tsayawa sana’a ko aiki daya ba.
Yace misali idan akwai gona a kusa da inda kake, sai ka dan yi noma dan samun saukin rayuwa.
Ya karkare da cewa ya kamata mutane su samarwa kansu mafita.