Sunday, March 23
Shadow

Akwai matsin tattalin arziki a kasarnan dan haka kada ku tsayawa sana’a ko aiki daya, ku raba kafa dan samun saukin rayuwa>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa ‘yan Najeriya shawarar cewa su raba kafa, kada su tsayawa sana’a daya.

Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na ChannelsTV.

Yace ba zai yiyu mutum ya tsayawa sana’a ko aiki daya ba.

Yace misali idan akwai gona a kusa da inda kake, sai ka dan yi noma dan samun saukin rayuwa.

Ya karkare da cewa ya kamata mutane su samarwa kansu mafita.

Karanta Wannan  Ranar Da Aka Karɓe Ka A Cikin Kwankwasiyya Daga Ranar Za Ka Fara Kirga Asara, A Cire Maka Hula Zanna Ta ₦30,000 A Sa Maka Jar Hula Ta ₦1000, Inji King Indara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *