
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa, Akwai wadanda suka rika yabon tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa shi mutumin kirki ne kuma babu shugaba Kamarsa a lokacin yana kan mulki.
Yace amma yana sauka daga mulki kuma suka juya suna zaginsa.
Ya bayyana hakane a wajan Taron Tunawa da marigayi Raymond Dokpesi mamallakin tashar talabijin ta AIT da gidan Radion Raypower da kamfanin Daar Communications.
Ya jinjinawa marigayin da kokarin bude gidan Talabijin me zaman kansa na farko a Najeriya.