Monday, December 16
Shadow

Akwai yiyuwar a yi fama da wahalar man fetur yayin da kungiyar NUPENG ke shirin bin kungiyar kwadago itama ta yi yajin aiki

Kungiyar ma’aikatan man fetur ta NUPENG ta umarci membobinta da su shiga yajin aikin sai mama ta gani wanda za’a fara a gobe Litinin.

Sakataren Kungiyar, Mr Afolabi Olawale ne ya bayyana haka inda yace kungiyar tasu zata bi umarnin yajin aikin.

Kungiyoyin NLC da TUC dai sun bayyana aniyar shiga yajin aiki a gobe litinin wanda sai abinda hali yayi kan neman gwamnati ta kara mafi karancin Albashi.

Wannan mataki na NUPENG dai zai iya jefa da yawa daga cikin ‘yan Najeriya cikin matsalar wahalar man fetur.

Karanta Wannan  Kai Tsaye Daga Babbar Kotun Tarayya Dake Kano, Inda Ake Yanke Hukunci Kan Shari'ar Masarautar Kano A Yanzu Haka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *