
Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin ya gana da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jiya.
Bayan ganawar tasu a yayin da yake ganawa da manema labarai an tambayeshi ko haka na nuna cewa zai koma APC ne?
Sai ya kayar da baki yace Yanzu ba lokacin wannan maganar bane, ya je ya gaishe da shugaba Tinubu ne sannan aun gana akan lamuran kasa, saidai yace abune mai yiyuwa ya iya komawa APC din.
Ya kara da cewa hadin kai da zaman lafiyar Najeriya shine gaba da komai kuma ba abin mamaki bane ganinsa a fadar shugaban kasar.