Da farko dai gaban mace kamar roba yake wanda zai iya budewa yayi fadi yayin da aka saka abu a cikinsa sannan idan an cire abin zai iya komawa ta tsuke.
Sannan a tsarin likitanci abubuwa 2 ne kawai ke sanya gaban mace ya bude ko ya saki ya daina tsukewa yanda ya kamata, sune shekaru da kuma haihuwa.
A yayin da girma ya kama mace ko ta yi shekaru masu yawa, gabanta zai saki zai daina tsukewa yanda ya kamata.
Mafi yawan masana ilimin kiwon lafiya sun bayyana cewa mata kan fara jin cewa gabansu ya fara saki a yayin da suka haura shekaru 40 a Duniya.
Hakanan a yayin da mace ta haihu,shima gabanta zai saki, yawan haihuwar da mace take yi,yawan budewar da gabanta zai rika yi kamar yanda masana ilimin kimiyyar lafiya suka sanar.
Alamomin da mace zata ji ko ta gani tasa gabanta ya bude sun hada da:
Raguwar jin dadin jima’i: A yayin da gaban mace ya fara budewa a dalilin yawan haihuwa ko yawan shekaru, zata fara rage jin dadin jima’i
Ramewa ko kankancewar fatar Gaba: A yayin da gaban mace ya bude, zata ga fatar gabanta watau lebatunnan guda biyu sun rame ko sun kankance.
Bushewar gaba: Budewar gaban mace yakan sa mace ta daina kawo ruwan ni’ima inda gabanta zai koma yana bushewa.
Kasa Rike Fitsari: Ga wasu matan a yayin da gabansu ya fara saki, zasu fara kasa rike fitsari wasu ma har suna iya fara yoyonsa.
Jin zafi yayin jima’i: A yayin da gaban mace ya bude, zata rika jin zafi yayin jima’i saboda ba zata rika kawo ruwan ni’ima kamar yanda tana budurwa ba da sauran matsaloli.
Fitar Ruwan Gaba: A yayin da gaban mace ya bude, wasu matan kan iya fuskantar fitar ruwa ta gabansu.
Allah ne mafi sani.
A taimaka a fadamin sahihancin wannan magana da ke cikin wannan post.
https://www.lafiyata.com.ng/2024/10/maganin-matsi-na-asibiti-tiyatar.html
Nagode admin
Salam Zee Sani, a iya binciken mu, bayanan dake cikin wancan rubutu masu inganci ne.
Mungode