Friday, December 6
Shadow

Ya ake gane mace ta balaga

Ana gane mace ta balagane ta hanyar canje-canjen dake faruwa a jikinta.

Yawanci mata suna balaga ne a tsakanin shekaru 9 zuwa 13, Inda suke Riga maza balaga da shekaru 2.

Ga alamun dake nuna mace ta balaga kamar haka:

  1. Girman nonuwa: Nonuwan yarinya zasu fara girma suna kara fitowa wake suna girma.
  2. Zafin Nono: Saboda girman da suke yi, nonuwan yarinyar zasu Dan rika mata zafi ko kaikai.
  3. Warin Jiki: Saboda zuwan balaga, yarinya zata iya fara warin jiki.
  4. Fitar Gashi a Hamata da Gaba: Gashin hamatarta Dana gabanta zasu fara fita suna kara kauri suna murdewa.
  5. Fara Jinin Al’ada: Yarinya zata iya fara jinin Al’ada.
  6. Majinar Farji: Gaban yarinyar zai fara fitar da ruwa me yauki.
  7. Kurajen Fuska: Yarinyar zata iya yin kurajen fuska Saboda canjawar da jikinta take.
  8. Zata iya kara kiba kuma nauyin jikinta zai karu idan balaga ta so mata.
  9. Girman Kugu: Kugunta zai bugs ya kara girma.
  10. Tsukewar Murya: Muryarta zata kara sirancewa.
Karanta Wannan  Maganin yawan tunani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *