Wednesday, January 15
Shadow

Albasa na maganin sanyi ga budurwa

Eh! Albasa na maganin sanyi ga budurwa:

Albasa na da sinadaran dake maganin sanyi ga budurwa hadda ma sauran mata.

Hakana albasa na taimakawa jiki wajan daidaita yawan ruwan da ya kamata ya kasance a jikin mutum. Shi kuma sanyi yawanci yana samuwa ne a yayin da ruwa da bai kamata ba ya zauna a jikin mutum, da haka wannan ma wani amfani ne na Albasar.

Hakanan Albasa na karawa garkuwar jikin mutum karfi wanda wannan ma wata hanyace ta taimakawa waja maganin cutar sanyi.

Albasa na kuma taimakawa wajan gudanar jini a jikin mutum wanda shima wata hanyace ta samun lafiyar zuciya da kariya daga cutar shanyewa rabin jiki.

Karanta Wannan  Amfanin albasa a fuska

Ana iya yanka Albasa akan abinci ko kuma a tafasata a ruwan zafi a sha da ruwan, in anso ana iya hada su yaji kadan, ko tafarnuwa da sauran kayan miya.

Saidai a kiyaye, kada a yiwa Albasar cin wuce misali, a ci a hankali.

Hakanan ana amfani da Albasa da Tafarnuwa da Lemun tsami a hada a tafasa a yi amfani da ruwan, shima yana taimakawa matuka wajan maganin sanyi ga budurwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *