
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, Albashin da yake biyan direbobin Tankarsa ya fi na wanda ya kammala jami’a.
Dangote ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai inda yayi karin haske kan rikicinsa da Kungiyar NUPENG.
Ya kuma gayyaci direbobin NUPENG duk wanda bai da aiki ya je zai bashi aikin tukin.
Dangote yace Albashin Direban tankarsa ya nunka mafi karancin Albashin sau 4 wanda akalla zai kai sama da Naira dubu dari uku kenan.