Friday, December 5
Shadow

Albashin sanatocin Najeriya su 109 zai iya biyan Albashin Farfesoshi 4,708, Kowane sanata yana karbar Naira Miliyan 21.6 duk wata, yayin da kowane Farfesa kuma ke karbar Naira 500,000 duk wata

Rahoto yace Jimullar kudin da ake baiwa Sanatocin Najeriya 109 a duk wata da suka kai 2.354 sun isa a biya albashin farfesoshi 4,708.

Kudin da ake biyan sanatocin ba albashine kadai ba, hadda kudin kula da ofisoshinsu da na kula da mazabunsu.

An dade ana mahawara akan albashin ‘yan majalisa da malaman makaranta, Musamman Farfesoshi.

A kwanannan aka ga Professor Nasir Hassan-Wagini na jami’ar Umaru Musa Yar’adua University, Katsina yana sayar da kayan miya inda yace yana yi ne dan taimakon kansa.

Matsakaicin Albashin Farfesa Naira 500,000 ne a yayin da Sanatoci ke karbar Naira Miliyan 21.6 duk wata.

A shekarar data gabata, BBCHausa ta yi hira da Senator Kawu Sumaila wanda yace duk wata Naira Miliyan 21.6 ake biyansu.

Karanta Wannan  Bìndìgù Sama da Dubu uku sun bace a hannun 'yansandan Najeriya

A hirarsa da Daily Trust, Farfesa Dr Niyi Sunmonu na jami’ar Obafemi Awolowo University, Ile-Ife ya bayyana cewa tun shekarar 2009 sun kan albashi daya ne ba kari in banda shakarar data gabata da aka musu karin kaso 35 cikin dari a matsayin farfesoshi wanda kuma ba farfesoshi ba aka musu karin kaso 25 cikin 100.

Yace gaba daya albashin Farfesa Naira N700,000 ne a wata amma bayan an cire haraji yakan koma Naira N500,000.

Yace a yanzu Farfesa ba zai iya canja motarsa ba ko kuma ya karbi bashin Naira Miliyan 10 ko 15 ba saboda albashin yayi kadan.

Yace a shekarar 1960, farfesoshi ne ma’aikatan da aka fi biyan Albashi cikin ma’aikatan Gwamnati.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon abin ban mamaki: Wata tsohuwar malamar Jinya(NURSE) tace sukan canjawa mata jarirai bayan sun haihu, wani lokacin ma sukan dauke Jariri su ajiye ma me jego Mattaccen Jariri, su sayar da natan

Yayi kiran gwamnati data inganta Albashin farfesoshi da sauran malaman makaranta dan inganta aikin da sakawa matasa karfin gwiwar yinsa.

Shima Prof. Balarabe Abdullahi na jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria (ABU) yace Albashinsa baya iya daukar dawainiyarsa.

Ya yi gargadin idan ba’a gyara ba, aikin koyarwa zai iya zama bashi da sha’awa a wajan matasa ko kuma su rika tserewa zuwa kasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *