Wani sakon WhatsApp ya bayyana wanda rahotanni suka bayyana cewa na Janar Muhammad Uba ne yake magana da sojojin dake kokarin cetoshi.

An ji yana fadar ceww chajin wayarsa ya kusa karewa.
Sakonsa na karshe shine wanda yake fadin cewa ya ji karan jirgi zai fita fili dan a ganshi amma daga nan ba’a sake jin duriyarsa ba.
Bidiyo dai ya bayyana yanda tsageran dajin suka kamashi.