
Rahotanni daga Daura na cewa, ana ci gaba da baiwa Kabarin Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kulawa.
A ranar da aka binne tsohon shugaban kasar, Kasa ce kadai aka gani akan kabarin nashi.
Saidai a yayin da mutane ke ci gaba da zuwa gaisuwa, an ga an kara sabuntashi an dan daga ginin.
Daga baya kuma bayan zuwan shugaban kasar Gambia, an ga an sake daga ginin kabarin sama sosai.
Muna fatan Allah ya jikan Buhari da sauran ‘yan uwa musulmi.