
Paul Pogba ya saka hannun yarjejeniya da kungiyar AS Monaco.
Zai bugawa kungiyar wasa na tsawon shekaru 2 zuwa shekarar 2027.
Hakan na zuwane bayan da ya kammala dakatarwar shekaru 2 da aka masa bayan samunshi da ta’ammuli da miyagun kwayoyi.
Da farko an yanke masa dakatarwar shekaru 4 amma daga baya aka mayar dashi shekaru 2 bayan ya daukaka kara.
Saidai Pogba a yayin da yake sakawa AS Monaco hannu ya fashe da kuka inda aka rika bashi baki.