Sunday, March 23
Shadow

Kuma Dai:Bayan karar data kai majalisar Dinkin Duniya, Sanata Natasha Akpoti ta sake komawa kotu kan dakatarwar da aka mata inda kotun tace majalisa ta mayar mata duka hakkokinta a matsayin Sanata idan ba haka ba zata daure Sanata Akpabio a gidan yari

Bayan korafin data kai majalisar Dinkin Duniya, Sanata Natasha Akpoti ta sake kaiwa kotu korafi kan dakatar da iymta da aka yi daga majalisar Dattijai.

Sanata Natasha Akpoti ta kai karar magatakardar majalisar, da gaba dayan majalisar, da kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio, da kuma shugaban kwamitn da’a na majalisar Sanata Neda Imasuem wanda shine ya bayar da shawarar a dakatar da ita.

Majalisar dai ta dakatar da sanata Natasha Akpoti na tsawon watanni 6 inda ta kwace motar da aka bata a matsayin sanata sannan aka janye mata jami’an tsaron dake kula da lafiyarta, hakanan an hanata zuwa kusa da majalisar.

Saidai wannan sabuwar dokar ta kotu tace tana umartar majalisar data dawowa da Sanata Natasha Akpoti da duka hakkokin a matsayinta na sanata.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ina masu neman tafsirin malam Attalili Attagazuti, to gashi

Babbar kotun ta gwamnatin tarayya tace ko da a baya ta hana majalisar ta ci gaba da binciken sanata Natasha Akpoti har sai an kammala sauraren karar data shigar gabanta amma majalisar ta yi kunnen uwar shegu.

A wannan karin, kotun tace idan majalisar ta ki yiwa umarninta biyayya, zata tabbatar ta hukuntata ta hanyar kulle kakakin majalisar a gidan yari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *