
Wannan Bidiyon ya nuna yanda wani ruwa me karfi ya tafi da sojan Najeriya yayin da ya je tsallaka wata kwata.
Da alama dai an kammala ruwan sama ne ruwan na gudu sosai shi kuma ya je tsallakawa, saidai bai samu nasarar tsallakawar ba inda ruwan ya tafi dashi.
Mutanen dake wajan sun yi yunkurin tseratar dashi amma abu ya faskara.