
Wata kungiya me suna GMI a takaice ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya dauki matakai kan tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi kan kalaman da yayi na cewa Talakawa au daina yadda ‘yan siyasa da basu wuce mutane dubu 100 ba na sacw dukiyar Najeriya.
Amaechi yace Mutanen Najeriya miliyan sama da 200 ne dan haka bai kamata su bari ‘yan siyasar da basu wuce mutane dubu 20 zuwa 100 ba suna sace dukiyar kasarnan ba.
Saidai a sanarwar kungiyar ta bakin shugaban ta, Samaila Musa tace wadannan kalamai na Amaechi zasu iya kawo taahin hankali da zuga talakawa.
Kungiyar ta yi kiran kada talakawa musamman matasa su saurari Amaechi inda tace su kaucewa yin amfani da karfi wajan canja gwamnati, su yi amfani da karfin kuri’arsu.
Hakanan ta yi kiran gwamnatin Tarayya ta dauki mataki kan Amaechi.