
Tauraron fina-finan Hausa, Saheer Abdul da ya je Madina, ibada da sayar da garin Danwake yace da yawan wadanda ke aika masa da neman ya taya su da addu’a matane.
Yace kuma yawanci suna cewa ne ya nema musu addu’ar Allah ya basu mazajen aure wasu kuma suna kiran ya taya su da addu’ar Allah yasa su samu zaman lafiya da mazansu.
Yace irin labaran da matan ke bashi akwai ban tausai.
Ya sha Alwashin taya su da addu’a.