Mata 3 ‘yan Najeriya da da aka kama a kasar Saudiyya aka tsare, tsawon watanni 10 bisa zargin safarar miyagun kwayoyi an sakesu bayan an gano basu da laifi.
Kakakin Ministan harkokin waje, Kimiebi Ebienfa ya tabbatar da hakan.
A watan Maris na shekarar 2024 ne aka kama matan a filin jirgin sama na Prince Muhammad Bin Abdulaziz dake Madina.
Matan sune, Hadiza Abba, Fatima Umate Malah, da Fatima Kannai Gamboi.
An kama su ne biyo bayan kama wasu ‘yan Najeriya biyu da hodar Iblis.
An kamasu ne bisa zargin cewa sun taimakawa masu safarar miyagun kwayoyin.
Lamarin ya dauki hankula sosai a kasashen Najeriya da Saudi Arabian inda Najeriya ta shiga tsakani har aka sakesu.
Bayan sakinsu, an mikasu ga ofishin jakadancin Najeriya dake kasar ta Saudiyya inda jakadan Najeriya a kasar Saudiyyan, Ambassador Muazam Nayaya ya karbesu.
Yanzu haka ana shirya musu yanda zasu dawo gida Najeriya.