
Tauraruwar fina-finan Hausa, ta bayyana cewa, ta bar harkar film saboda ba riba.
Tace shekarunta 20 tana harkar film amma bata ajiye komai ba.
Ta bayyana cewa yawanci dubu 5 ake biyansu idan suka yi fim.
Ta kara da cewa, yanzu haka bata da inda zata zauna sannan bata da sutura kuma abinci ma yana musu wahala.
Tace da zata samu Mijin aure, zata yi aure ta huta.