
Labarin wata mata me ciki da ta rasu a babban asibitin garin Minna na jihar Naija, Babbangida Aliyu General Hospital yayin da ake mata aiki ya yadu sosai a kafafen sada zumunta.
Mijin matar ne ya wallafa labarin a shafinsa inda labarin ya watsu sosai.

Yace an farawa matar tasa aiki da wutar Nepa, sai aka dauke.
Ashe Janaretan ba man fetur, sai da aka je aka siyo mai aka zubawa janaretan amma yaki tashi, yace sai da aka je aka kira makanike.

Yace a yayin da ake duk wannan abin, matarsa na cikin dakin tiyatar an fara mata aiki ba’a gama ba.
Danga nan ne ta rasu.

Muna fatan Allah ya jikanta