Wednesday, November 19
Shadow

Ji yanda aka kama wasu ‘yan Najeriya na shirin shiga kasar Ingila da wani yaro da suka sata daga Najeriya

Hukumomin kula da iyaka na kasar Ingila sun kama wasu mutane biyu mace da namiji daga Najeriya wanda suka yi yunkurin shiga kasar da wani yaro da aka yi amannar satoshi suka yi.

Hukumomin kula da iyakar a filin jirgin sama na Manchester sun tsargu da mutanen bayan ganin yanda suke tafiya da yaron.

Ko da aka bincikesu sai namijin me suna Raphael Ossai yace shine mahaifin yaron sannan kuma matar da suke tare Oluwakemi Olasanoye wai itace mahaifiyar yaron.

Saidai da bincike yayi tsanani, an gano cewa, akwai kuma wata takardar haihuwa data bayyana wata mata dake zaune a kasar ta Ingila wadda aka bayyana da cewa itace mahaifiyar yaron.

Karanta Wannan  Dalla-Dalla: Yaronnan dan shekaru 18 da ya dirkawa mata 10 ciki yayi bayanin dabarar da yakewa matan suna yadda dashi

Tuni dai aka kama matar da namijin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *