
Wani tsohon mataimakin gwamna a kasar Kenya ya koma sana’ar sayar da itace.
Sunansa Caleb Amaswache kuma yana wannan sana’a ne a garin Luanda.
Ya roki shugaban kasar kenya, William Ruto da ya bashi aikin yi.
Yace a lokacin yana mataimakin gwamna, komai gwanin ban sha’awa amma yanzu babu wanda ke son daukar wayarsa ma.