
Al’umma Jihar Kano sun yi ikirarin cewa gayyatar da babban Sifetan ‘yansanda ya yi wa Sarki Sanusi wani bangare na shirin kafa dokar ta-baci a Jihar.
Hakan na zuwa ne biyo bayan rahotannin da ke cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a hukumance, zuwa ofishin ta dake Abuja domin bincike kan wani yamutsu da aka samu a lokacin bukukuwan Sallah.
Wasu ‘yan jihar da suka yi magana kan kama Usman Sagiru dan shekara 20 a ranar Lahadi, 30 ga Maris, 2025 da ke Sharifai Quarters dangane da zargin kisan wani dan banga a tawagar Sarki Sanusi Lamido Sanusi na biyu bayan Sallar Idi, sun bayyana cewa ba za su iya alakanta lamarin da gayyatar Sarki ba.
Takardar gayyata mai kwanan wata 4 ga Afrilu, 2025, kuma mai dauke da sa hannun CP Olajide Rufus Ibitoye, kwamishinan ‘yan sanda (Ayyuka), an bayar da shi ne a karkashin umarnin babban sufeton ‘yan sanda na ƙasa
Wasikar ta bukaci Sarki Muhammadu Sanusi II da ya kai kansa ga hedikwatar hukumar leken asiri da ke Abuja a ranar Talata 8 ga Afrilu, 2025 da karfe 10 na safe.