Danyar Albasa na da matukar amfani, ga wasu daga cikinsu kamar haka:
Tana dauke da sinadarin Vitamin C wanda yake taimakawa kara karfin garkuwar jiki.
Hakanan tana dauke da abinda ake cewa Antioxidant me karfi sosai wanda ke taimakawa wajan yaki da ciwukan dake kawo saurin tsufa.
Hakanan tana taimakawa wajan rage kiba.
Tana taimakawa wajan kare zuciya.
Tana kara karfin kashi.
Tana taimakawa kaucewa cutar daji watau Cancer.
Tana kara lafiyar fata.
Tana kara kaifin kwakwalwa.
Saidai cin dafaffiyar Albasa yafi amfani saboda danyar zata saka:
Warin Baki.
Zata iya bayawa wasu ciki.
Zata iya saka rika yin tusa.