Tafarnuwa da man Zaitun suna da matukar Amfani sosai musamman ga lafiyar zuciya.
Suna taimakwa wajan gudanar jini sosai dan haka shansu a cikin abinci yana taimakawa lafiyar zuciya, kuma yana zama garkuwa ga cutar shanyewar rabin jiki.
Ana iya amfani da Man Zaitun da Tafarnuwa wajan gasawa ko dafa Kaza da nama da sauran abubuwanda ake gasawa, ana kuma iya cinsa da taliya, makaroni ko shinkafa.
Ana iya yin amfani da Man Zaitun da Tafarnuwa kuma ana iya kara wani abin amfanin kamar ganyayyaki haka.
Man Zaitun kuma yana kare mutum daga cutar siga da cutar hawan jini, yana kuma kawar da alamun tsufa a jikin fata.