Wednesday, January 15
Shadow

Amfanin tumatir a jikin mace

Tumatir na daga cikin manyan abinci ko sindarin hada abinci da ake amfani dashi a Duniya dama Najeriya, Musamman kasar Hausa.

A wannan rubutu, zamu yi bayanin Amfanin Tumatir ga jikin mace:

Lafiyar Zuciya: Tumatir na taimakawa wajan karawa zuciyar dan Adam Lafiya sosai idan ana shan sa. Yana rage hadarin kamuwa da cutar ta zuciya sosai.

Yana Zama Rigakafi ga cutar Daji: Shan Tumatir na zama rigakafi ga cutar daji ko ace Cancer, hakanan yana taimakawa ga masu neman haihuwa.

Kara Lafiyar Ido: Tumatur na kara lafiyar Ido, musamman masu fama da matsalar ido, idan suna shan Tumatir zasu samu karfin gani musamman da dare.

Karanta Wannan  Amfanin ganyen gwanda

Yana da Matukar Amfani ga masu fama da cutar Sugar.

Tumatir Na maganin kumburin Jiki.

Tumatir na Taimakawa sosai wajan karawa garkuwar jikin mutum karfi.

Tumatir na taimakawa wajan baiwa fata kariya daga kunar rana wadda ake kira da sunburn. Hakanan a wani kaulin yana taimakawa wajan samun shekin fata.

Hakanan Tumatir na karawa fata Haske, Musamman wadanda ke dadewa suna aiki a rana, Tumatir na taimakawa wajan sanya fata ta yi haske sosai.

Tumatir na karawa kashin mutum lafiya da karfi.

Tumatir na baiwa jikin mutum kariya daga abubuwan dake kawo saurin tsufa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *