
Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana rashin jin daɗinta kan bayar da umarnin kama Hamdiyya Sidi Sharif da wata kotun Majistare da ke jihar Sokoto ta bayar.
A ranar 10 ga watan Yuli ce wata kotun majistare da ke zamanta a Wurno a yankin Gwiwa ta bayar da umarnin kamo mata Hamdiyya saboda matashiyar ba ta samun damar halartar zaman kotun ba a ranar 9 ga watan Yulin.
A wata sanarwa da Amnesty ta fitar, ta bayyana cewa Hamdiyya ba ta samu zuwa kotun ba ne saboda “ba ta jin daɗi.”
“Muna kira da a janye wannan umarnin na a kama ta har sai an kammala sauraron buƙatar gudanar da shari’ar ba tare da ta bayana ba wanda lauyoyinta suka shigar.”
Hamdiyya na fuskantar shari’a ne daga gwamnatin jihar Sokoto bisa zarginta “amfani da munaman kalamai da tunzura jama’a” kan gwamnatin na jihar Sokoto.