Monday, March 17
Shadow

An ɗage taron mahaddata Qur’ani da aka shirya yi a Abuja

Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an ɗage taron mahaddata al-Qur’ani da ake yi wa laƙabi da Qur’anic Convention a Turance da ya rage ƙasa da mako biyu a gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya.

An dai saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 da ranar da za a yi taron da ake sa ran zai samu mahalarta waɗanda mahaddata Qur’ani ne sama da dubu 60 daga ciki da wajen Najeriya.

Wani ɗan kwamitin tsara taron wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa “tun daren jiya Alhamis aka ɗage yin wannan taro.

Sai dai kuma majiyar ba ta tabbatar wa da BBC haƙiƙanin dalilin da ya sa aka ɗage taro ba da kuma yaushe ne sabon lokacin da za a yi taron a nan gaba.

Karanta Wannan  Da Mahaifiyata ta mutu, An bani Kyautar Naira Miliyan dari biyar amma naki karba dan tsare mutunci na>>Inji Shugaban EFCC

“Ana sa ran sai bayan Ramadan.” In ji majiyar.

Manufar taron

Taron dai wanda tuni allunan tallansa suka cika manyan titunan birnin Abuja ya kankane kafafen watsa labarai da na zumunta, inda wasu ke yabo wasu kuma ke kushe shi.

Da ma tun kafin yanzu batun taron na mahaddatan ya janyo muhawara, inda wasu ke sukar kalmar da aka yi amfani da ita ta “festival” da ke nufin da “biki”, sannan wasu ke dangantaka al’amarin da siyasa, wasu kuma suke kallonsa a matsayin wani abu baƙo a addinin Musulunci.

Manufar taron dai kamar yadda shafin tsara taron ya ce shi ne fito da irin jajircewar da mahaddata al-qur’ani suka yi shekara aru-aru.

Karanta Wannan  Labari Me Dadi: EFCC sun kwato kudade masu yawan da basu taba kwatowa ba a hannun barayin gwamnati

“Al’ummar Najeriya daga sassa da ƙabila daban-daban na ƙasar sun sadaukar da rayuwarsu wajen haddace Qur’ani a ɗaruruwan shekaru” In ji shafin da ke tsara taron.

Saboda haka wannan taron zai zama wani dandamali na karrama makaranta da marubuta al-qur’ani mai girma. Sannan wata mahaɗa ce da ke nuna yadda al’adu da ƙabilun Najeriya daban-daban ke karanta da mu’amala da Qur’ani da irin karin harshensu sannan bisa al’adunsu.” In ji shafin.

Shafin ya kuma lissafa ƙarin wasu muhimman abubuwan da za a yi a lokacin taron kamar haka:

  • Karrama mahaddata Al-Qur’ani: Taron zai fito da irin jajircewa da ƙoƙarin mutanen da suka haddace da kuma waɗanda suke iya rubuta al-qur’ani baki ɗaya.
  • Haɗin Kai: Taron zai tattara al’umma daga sassa da ƙabila daban-daban na Najeriya da ke mu’amila da littafi mai tsarki.
  • Zaburar da Ƴanbaya: Wata manufar ta wannan taro ita ce sanya wa yara sha’awar haddace al-qur’ani tunda ƙuruciyarsu, ta hanyar tallata irin nasarar da mahaddatan suka yi domin ganin al’adar haddace Qur’ani ta ɗore.
  • Fito da basirar Mahaddata: A lokacin taron, za a fito da irin basira da kaifin hadda da kuma jajricewar da mahaddata ke da ita.
Karanta Wannan  Allah Ya Yiwa Mahaifiyar Tsohon Shugaban Najeriya Marigayi Umaru Musa Yar'adua Hajiya Dada Rasụwa Yanzun Nan A Unguwar Yar'adua Da Ke Cikin Garin Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *