Tuesday, January 7
Shadow

An baiwa Tinubu Shawarar a tsaurara tsaro a iyakokin Arewa

Tsaffi janarorin soji da tsaffin jakadu da masana harkar tsaro sun baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar a tsaurara tsaro a iyakokin Arewa dake da iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Hakan na zuwane yayin da dangantaka ke kara yin tsami tsakanin Najeriya da kasar ta Nijar inda kasar Nijar din ta zargi cewa Kasar Faransa ta baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu makudan kudade dan a girke sojojin Faransa a iyakokin Najeriya da Nijar.

Saidai a martanin me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, yace babu sojojin Faransa a Najeriya.

Ribadu ya kara da cewa kuma Najeriya ba zata canja huldar jakadancin dake tsakaninta da kasar Faransa da Amurka da Rasha ba saboda rashin jituwar dake tsakanin Faransar da Kasar Nijar.

Karanta Wannan  Wani abu da ba'a san ko menene ba ya Bugi jirgin saman Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima inda ya lalatashi yayin da yake kasar Amurka

Ana ta ci gaba da kai ruwa rana tsakanin Najeriya da Nijar din inda koda a kwanannan saida kasar ta Nijar ta dawo da ‘yan Najeriya su sama da 700 gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *