Friday, December 5
Shadow

An bayyana abinda ke ta’azara matsalar tsàrò a Najeriya

A Najeriya masana lamuran tsaro na ci gaba da bayyana albarkacin baki kan samun jami’an tsaro da suke safarar makamai ga ƴanbindiga.

Masana suna cewa rashin ɗaukar matakan hukunta jami’an tsaron da aka samu da laifin safarar makamai ga ƴanbindiga, da kuma biyan jami’an tsaron ƙasar albashin da bai taka kara ya karya ba, na daga cikin abubuwan da ke taka rawa wajen ci gaba da samun karuwar wasu baragurbin jami’an tsaron da ke safarar makamai ga mayaƙan Boko Haram da ‘yan fashin daji.

Barista Audu Bulama Bukarti, lauya kuma masani lamuran tsaro ne a nahiyar Afirka, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Najeriya na sakaci da lamuran da suka shafi tsaro da suka haɗa da rashin bibiyar yadda ake kashe kuɗaɗe a ɓangaren da ma yin biris da makomar sojoji da sauran masu aikin samar da tsaro a kasar.

Karanta Wannan  Ji Yadda ma'aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsìraìcìn abokan aikinsa mata a Najeriya, ya nadi Bidiyo 400

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *