
A yayin da ake fuskantar zaben shekarar 2027 an bayyana dan siyasa daya tilo da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke shakkar karawa dashi a shekarar 2023.
Wani dan kasuwa, Stephen Akintayo ne ya bayyana hakan inda yace Peter Obi na jam’iyyar Labour Party ne ke kayarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gaba.
Ya bayyana cewa, idan aka hada Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin mataimakinsa, Tinubu ba zai iya bacci ba.