
Rahotanni sun bayyana cewa akwai gwamnoni 2 na jam’iyyar PDP dake son komawa jam’iyyar ADC.
Na farko shine Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Rahoton yace akwai yiyuwar gwamnan ya koma ADC a kowane lokaci. Tuni dai dangantaka tsakanin Gwamna Seyi Makinde da Wike ta yi tsami.
Hakanan akwai gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad.
Shima dai Gwamna Bala Dangantaka tsakanin sa da Gwamnatin tarayya da Wike ta yi tsami.
A baya dai yace ana zarginshi da hannu a matsalar tsaro ne saboda ya ki komawa jam’iyyar APC.