Jagoran jam’iyyar NNPP, mai mulkin jihar kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana takaicinsa kan yadda ya ce gwamnatin tarayya ta raba kayan tallafin shinkafa ga Jihohi 35 duk ta hannun Gwamnonin su, amma ban da Jihar Kano.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Jagoran Kwankwasiyyar ya yi zargin cewa gwamnatin tarayyar ta miƙa kason jihar Kano hannun jiga-jigan jam’iyyar APC, wanda a cewarsa hakan ya saɓa wa dimikraɗiyya.
”Wannan babban cin fuska ne ga dimokradiyya da kuma tsarin mulkin ƙasar mu. Wannan mataki dai nuna ɓangaranci ne da ya wuce gona da iri,” in ji jagoran jam’iyyar NNPP.
Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasar ya gagguata dakatar da abin da ya kira karan-tsaye wa tsarin dimikraɗiyyar ƙasar.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NNPP ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ya ce an aike da daraktocin hukumar DSS har guda uku zuwa jihar Kano, tare kuma da sauya su duka cikin mako biyu zuwa uku, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga tsaron jihar.