Wednesday, October 9
Shadow

Gyaran nono lokacin yaye

A yayin da jaririnki ya daina shan nono kika yayeshi. Nononki zai iya daukar kusan kwanaki 5 zuwa 10 yana dan kumburi nan da can, hakan ba matsala bane,duk da ba kowace mace ce ke fuskantar wannan matsala ba.

Idan hakan ya faru dake, zaki iya rika yiwa nonon naki tausa sannan zaki iya rika matso ruwan nonon kadan-kadan.

Hakanan ga wanda nonuwan ke zafi bayan kammala shayarwa, ana iya rika dira ruwan sanyi ko a nade kankara a tsumma me kyau a rika dorawa akan nonon.

Yana da kyau kuma a rika shan ruwa ko abinda ya danganci riwa.

Ana iya shan magungunan rage radadin ciwo irin su Ibuprofen.

Karanta Wannan  Gyaran nono da man kadanya

Sannan maganar gyaran nono ya koma kamar yanda yake kamin ki dauki ciki kuwa, daya daga cikin hanyoyin da ake samun nasarar hakan shine ta hanyar motsa jiki.

An fi son motsa jikin da zai rika motsa kirjinki kamar ki kwanka akan gadon bayanki ki rika dago saman jikinki kadai ba tare da kafa ba, da press up ko push ups da sauransu.

Hanya ta biyu wajan dawo da armashin nononki bayan gama shayarwa itace ta yiwa nonuwan naki tausa, zaki iya amfani da hannuwanki kina yiwa nonuwan naki tausa daga lokaci zuwa Lokaci.

Hanya ta uku da ake amfani da ita wajan dawo da karsashin nono bayan kammala shayarwa itace yin tiyata wadda tana da hadari da kuma tsada.

Karanta Wannan  Gyaran nono a sati daya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *