
Wata mata shahararriya a kafafen sadarwa me suna Raye ta koka da cewa an cire mata harajin naira 487,500 bayan da ta kashe Naira Miliyan 6.5 wajan sayayya.
Wannan koke nata na zuwane kwanaki kadan bayan da Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za’a fara cirewa mutane Haraji ranar 1 ga watan Janairu.
Ta wallafa rasit din harajin da aka cire mata wanda ya dauki hankula sosai.

Da yawan ‘yan Najeriya dai na ta kokawa da maganar Harajin da Gwamnatin tarayya ta kawo.