Friday, December 5
Shadow

An ga fastocin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a kafafen sada zumunta, Ya mayar da martani

Rahotanni sun bayyana fastocin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a kafafen sada zumunta inda aka ga yana neman tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

An ga fastocinne a kafar Instagram.

Shafin da ya wallafa labarin na dauke da sunan tsohon shugaban kasar ne inda ya soki gwamnati me ci.

Saidai da aka Tambayi kakakin Jonathan din me suna Ikechukwu Eze ya musanta cewa ba Jonathan ne ya ke yakin neman zabeba, bashi ma amfani da shafin Instagram.

Ba wannan ne karin farko da ake amfani da sunan tsohon shugaban kasar ana nuna yana neman sake tsayawa takarar shugaban kasa ba, ko da a shekarar 2023 ma an samu wasu suka rika amfani da sunansa suna cewa ya fito takarar shugaban kasa.

Karanta Wannan  Wani Magidanci ya je ofishin 'yansanda na jihar Kano inda yace zai kara aurene shine ya baiwa matarsa Naira Miliyan 2 toshiyar baki, shine yake neman shawara ko hakan ya sabawa doka?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *