Masana kimiyya a nahiyar Turai sun gano ƙanƙarar da watakila ake ganin ita ce mafi daɗewa a duniya a yankin Antarctica.
Tawagar masu binciken ta haƙo silindar ƙanƙarar mai tsawon kusan kilomita uku wanda ke ɗauke da tsohon kumfa da kuma ɓurɓushi da aka daina ganin irinsa tun fiye da shekara miliyan guda.
Masanan na fatan cewa yin nazarin tarihin yanayin zafi da matakan iskar gas zai taimaka musu wajen hasashen sauyin yanayi a nan gaba.
Tuni dai masu binciken suka yayyanka ginshiƙin ƙanƙarar zuwa sassa masu tsayin mita ɗaiɗai domin faɗaɗa bincike a cibiyoyin bincike a faɗin nahiyar Turai.