Tuesday, May 19
Shadow

An gano ƙanƙara mai shekara fiye da miliyan ɗaya a duniya

Masana kimiyya a nahiyar Turai sun gano ƙanƙarar da watakila ake ganin ita ce mafi daɗewa a duniya a yankin Antarctica.

Tawagar masu binciken ta haƙo silindar ƙanƙarar mai tsawon kusan kilomita uku wanda ke ɗauke da tsohon kumfa da kuma ɓurɓushi da aka daina ganin irinsa tun fiye da shekara miliyan guda.

Masanan na fatan cewa yin nazarin tarihin yanayin zafi da matakan iskar gas zai taimaka musu wajen hasashen sauyin yanayi a nan gaba.

Tuni dai masu binciken suka yayyanka ginshiƙin ƙanƙarar zuwa sassa masu tsayin mita ɗaiɗai domin faɗaɗa bincike a cibiyoyin bincike a faɗin nahiyar Turai.

Karanta Wannan  Da Mu Da Kwankwaso Duk Tinubu Muka Yi Wa Aiki A Zaben 2023, Kuma Idan Har Kwankwason Da Na Sani Ne Zai Sake Sabunta Wannan Kwangilar A 2027, Inji Dan Bilki Kwamanda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *